23 Yuli 2023 - 07:10
Yeman Ta Sanar Da Dakatar Da Tattaunawa Da Saudiyya

Shugaban majalisar koli ta siyasar kasar Yemen ya sanar da dakatar da tattaunawa da kasar Saudiyya wadda ita ce jagorar kawancen kasashen Larabawa, sannan ya ce Amurka na kawo cikas ga wannan tattaunawar.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya nakalto daga tashar Al-Mayadeen cewa, a watan Janairun da ya gabata ne birnin San'a'a ya samu kudirin Saudiyya na cewa, a maimakon tsawaita wa'adin tsagaita bude wuta da kuma ba da damar sake fitar da man kasar Yemen, za a biya albashin ma'aikata na shekara guda a kan Riyal na Saudiyya.

A cewar sanarwar da tashar Al-Mayadeen ta fitar, Yemen "ta bukaci cire hannun Saudiyya daga fitar da man fetur na kasar Yemen da kuma karfafawa 'yan kasar ta Yemen hakkinsu na mallakar dukiyarsu."